Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya taya David Cameron murna game da lashe babban zaben kasar Birtaniya da ya yi tare da jam'iyyar sa.
A sakon da ya aika masa a jiya Juma'a, Mr.Li Keqiang ya ce a shekarun baya-bayan nan Sin da Birtaniya sun samu kyakkyawan ci gaba, musamman a fannin raya dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu.
Ya ce a matsayin su na manyan kasashen duniya, matakan da kasashen biyu ke dauka na zurfafa zumunci, da hadin gwiwa, da kuma kara cudanya da juna a cikin harkokin shiyya-shiyya da kasa da kasa, na haifar da alfanu ga jama'ar su, baya ga babban tasiri da hakan ke da shi ga dukkanin kasashen dake fadin wannan duniya.
Li Keqiang ya nanata cewa, Sin na fatan kara amincewa da juna, da kuma zurfafa hadin kai, da samun bunkasuwa tare, kana da kara raya dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin ta da kasar Birtaniya. Har wa yau Sin na fatan kara yawaita mu'ammala tsakanin firaministocin kasashen biyu a nan gaba, domin tattauna kan matakan da kasashen biyu za su dauka, na raya kai cikin hadin gwiwa. (Amina)




