Yayin tattaunawarsu, firaminista Li ya ce, a halin da ake ciki yanzu, ana raya tattalin arzikin Sin cikin sabon tsari yadda ya kamata, kamata ya yi a saba da wanna sabon yanayi, don inganta aikin yin gyare-gyare, da kawo kuzari ga raya shi, ta hakan, za a sanya tattalin arzikin kasar don ya samu matsaikaci ko saurin bunkasuwa.
A sa'i daya kuma, ya zama wajibi gwamnati ta tabbatar da inganta zaman rayuwar jama'a, da kawar da dukkanin damuwa ga masu sha'awar sana'o'i na gashin kansu, musamman ma ga matasa, don sa kaimi ga samar da adalci a zamantakewar al'umma, da inganta samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma tare.
Li Keqiang ya yi nuni da cewa, yanzu, gwamnatin Sin na kara bude kofa ga 'yan kasuwar kasashen waje.
A nasu bangare, wakilan kasashen waje sun bayyana taron tattaunawa na wannan karo wata dama ta kara fahimta, game da canja salon bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Kamfanonin ketare na kasashe waje na sa ran tashi tsaye don shiga cikin yunkurin aikin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, kuma suna fata za a raya tattalin arzikin Sin cikin dogon lokaci kuma yadda ya kamata.(Bako)