Bankin zuba jarin Turai (BIE) da bankin kasuwanci da ci gaban gabashi da kudancin Afrika (PTA Bank) sun kaddamar a ranar Talata da wani shirin ba da rance na kudin Euro miliyan 160 domin tallafawa zuba jari a wadannan shiyyoyi biyu na Afrika.
Kamar yadda wannan yarjejeniya da aka sanya wa hannu a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya ta tanada, kamfanoni na bangarorin da suka shafi abinci da noma, makamashi, masana'antu da sauran ayyuka za su samu damar daukar rance bisa darajar kudin wurin bisa tsawon shekaru bakwai ko wani rance kudi da dalar Amurka ko da Euro bisa tsawon shekaru 15 a wajen PTA Bank. (Maman Ada)