A Webank, Li Keqiang ya danna "Enter" a kan kamfuta, ta haka wani direba mai suna Xu Jun ya samu rancen kudi da yawansa ya kai RMB yuan dubu 35. Wannan ne karo na farko da bankin intanet mai zaman kansa na kasar Sin ya bayar da rancen kudi na farko. Li Keqiang ya bayyana cewa, ya yi farin ciki sosai, kuma ana karfafawa sha'anin hada-hadar kudi ta hanyar intanet. Ya ce, kamata ya yi Webank ya kara gudanar da harkokinsu a dandalin hada-hadar kudi, da samar da fasahohi ga kananan kamfanoni ko bankuna a kasar. Kuma ya kamata Webank ya bada rancen kudi ga kananan kamfanoni ko mutane, ta haka za a sa kaimi ga yin kwaskwarima kan tsarin hada-hadar kudi na gargajiya.
Kamfanoni 3 masu zaman kansu sun kafa Webank, jama'a za su iya samu rancen kudi a Webank ba tare da samun bayanai kan kudin shiga nasu ba. Bankin ya yi amfani da fasahohin kamfanin Tencent wajen tabbatar da matsayin mutane na iya biyan bashi, da bada rancen kudi gare su ta hanyar yin amfani da fasahohin tantance fuskokinsu. (Zainab)