Wannan kira an yi shi ne a yayin da rikicin al'umma a kasar Benin ya fara kamari tun cikin watan Satumba.
Jam'iyyun adawa, kungiyoyin kwadago da kungiyoyin fararen hula sun daga muryarsu domin bukatunsu da suka hada da ganin an tsaida ranar da ta dace ga zabubukan kasa. Musammun ma zabubukan kananan hukumomi da aka tsaida shiryawa kafin watan Disamban shekarar 2014, da kuma zabubukan 'yan majalisu da na shugaban kasar dukkansu a cikin watan Maris na shekarar 2015. (Maman Ada)