in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta horar da ma'aikatan jiyya na kasar Senegal fasahohin yaki da cutar Ebola
2015-01-21 15:44:33 cri

Da yammacin jiya Talata ne, aka shirya bikin kammala horaswa kan yadda za a fuskanci cututtuka masu yaduwa a kasar Senegal da ke yammacin Afirka.

A gun bikin kammala horo kan yadda za a shawo kan cututtuka masu yaduwa, wanda aka shirya a otel din King Fahd da ke birnin Dakar, hedkwatar mulkin kasar Senegal a jiya Talata, wani ma'aikacin jinya daga sojojin kasar Senegal mai suna Adama Gueye, ya bayyana kwarewar da ya samu yayin wannan kwas. Ya ce,

"An koya mana yadda ya kamata a rika wanke hannu kafin cin abinci, da kuma bayan an fito daga bayan gida, da yadda za a magance kamuwa da cututtuka masu yaduwa tsakanin iyaye mata da yaransu. Sannan nan an koya mana abubuwan da ya kamata mu ma'aikatan jiyya mu lura da su yayin da muke tuntubar wadanda suka kamu da cuta, musamman ma yadda za mu sa da cire tufafin kariya yadda ya kamata."

Horon da Adama Gueye ya samu horo ne na kwararru masu aikin jiyya uku, daga lardin Fujian na kasar Sin wanda aka shirya domin tallafawa ma'aikatan jiyya 100 dake birnin na Dakar. Kamar yadda Gueye ya fada, zai bi ka'idojin jinya da ya koya yayin wannan kwas, a cikin aikinsa na nan gaba.

Bugu da kari shi ma zai koya wa iyalinsa, da yaransa wadannan dabaru, domin su san yadda za su iya kare kansu idan an gamu da cututtuka masu tsanani kamar cutar Ebola.

Ko da yake hukumar kiwon lafiyar ta duniya WHO ta sanar da cewa, kasar Senegal kasa ce da ta kubuta daga cutar Ebola, amma kasancewar ta maras kyakkyawan tsarin kiwon lafiya, kuma jama'arta ba su da kwarewa wajen samun kariya daga cututtuka, da ma cudanyar mutane da yawa a yammacin Afirka, hakan ya sa har yanzu ake mai da hankali sosai kan shawo kan cutar Ebola.

Likita Abdou Thiam daya ne daga wadanda suka halarci wannan horo, yana kuma ganin cewa, abin da ya fi muhimmanci ga kasar Senegal shi ne, koya wa al'umma dabarun ba da kariya daga cutar Ebola. Ya kara da cewa,

"Bisa la'akari da yanayin da ake ciki a yammacin Afirka, ya kamata mutane su shiga irin wannan kwas na samun horo."

Domin tallafa wa kasashen da ke yammacin Afirka wajen yaki da cutar Ebola, kasar Sin ta tura kwararru zuwa kasashen Guinea, Liberia, Saliyo, Guinea Bissau, Mali, Ghana, Togo, Benin da kuma Senegal a karshen shekarar bara, domin ba da horon shawo kan cutar. Kwararru uku daga lardin Fujian na kasar Sin sun isa Senegal a ranar 3 ga watan nan, kuma za su ba da horo ga ma'aikatan jiyya fiye da 500, daga yankuna 10 dake dukkanin fadin kasar. Wakiliyar kungiyar WHO da ke Senegal Alimata Diarra-Nama ta jinjinawa wannan aikin da kasar Sin ke yi. ta ce,

"Ina farin cikin ganin yadda kasar Sin ke ba da horo ga ma'aikatan jiyya, wanda ya kasance kashi mafi muhimmanci game da samar da taimako a wannan fanni. Wannan horo kuwa zai karfafa kwarin gwiwar ma'aikatan jiyya, wajen kyautata karfinsu na ba da kariya daga cutar Ebola. A nan, ina so in yi gargadin cewa, wannan cuta ta Ebola ta riga ta haddasa mutuwar ma'aikatan jiyya fiye da 400. Don haka ina fatan, sauran kasashe za su yi koyi daga kasar Sin, da kuma kara ba da taimakon tinkarar cutar."

Rahotanni sun nuna cewa kafin wannan mataki, kasar Sin ta riga ta bai wa Senegal kayayyakin ba da kariya da darajarsu ta kai Yuan miliyan 5, wadanda suka hada da tufafin kariya, da na'urorin auna yanayin jiki, da dai sauran kayayyakin jiyya. Jakadan kasar Sin da ke Senegal Xia Huang ya bayyana cewa, kasar Sin ba za a dakatar da tallafin da take bayarwa ba. Ya ce,

"kasar Sin za ta hada kai tare da ku, domin yaki da cutar Ebola, kuma muna fatan taimaka muku wajen kafa kyakkyawan tsarin kiwon lafiyar jama'a, wanda zai kasance daya daga cikin ayyukan hadin kanmu."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China