in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar samar da taimakon gaggawa ga wadanda suka harbu da cutar Ebola ta ce an samu ragowa na adadin jama'ar dake kamuwa da cutar
2015-01-21 10:46:43 cri
A yayin da yake jawabi ga wani babban taro na MDD a game da nasarorin yunkurin tunkarar cutar Ebola da aka dauka a duniya, sabon shugaban hukumar MDD mai bayar da agaji a cikin gaggawa ga wadanda suka kamu da cutar Ebola, Ismael Ould Chiekh Ahmed yace yaduwar cutar a yanzu ya ragu matuka, musamman a kasashe 3 inda cutar ta yi kamari.

Ismael ya kara da cewar daga cikin kasashen ukku inda cutar ta fi kamari, kasar Liberia ta fi sauran kasashen biyu samun ragowar adadin yawan jama'ar dake harbuwa da cutar ta ebola, alal misali kididdiga na nuni da cewar a Liberia an samu ragowa daga yawan jama'a 300 a duk mako a watan Agustar bara ya zuwa mutane kasa da 10 kacal a duk sati a watan satumba

Hakazalika adadin yawan masu kamuwa da cutar Ebola a Saliyo da Guinea ya ragu matuka tun daga watan yuli da Agusta na shekarar bara. To amma Ismael ya ce a yayin da ake samun raguwar mutanen dake kamuwa da cutar sai kuma cutar ta yadu zuwa wasu wurare nesa da inda cutar ta bulla tun asali, hakan ya sa magatakardan MDD Ban Ki-moon daukar mataki na baiwa kasashe shawarwari da su kaucewa sakaci wajen yaki da cutar Ebola. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China