Wani mai magana da yawun hukumar tsaron kasar ta Koriya, ya ce Amurka ta dage cewa Koriyan ce ta yi kutse cikin na'urori masu kwakwalwa na kamfanin na Sony. Sai dai ya ce sam wannan zargi ba shi da tushe balle makama. Jami'in ya ce kamata ya yi Amurka ta amince da gudanar da bincike tare da Koriya ta arewa, domin tantance gaskiyar wannan lamari.
Kaza lika mahukuntan kasar sun bayyana sabon fim din da kamfanin na Sony ya fitar, a matsayin abin da ya sabawa dokokin kasa da kasa, tare da keta hurumin kasar Koriyan, dama dokokin da suka tanaji hana tsoma baki cikin harkokin gida na wata kasa.
A makon da ya gabata ne dai hukumar kula da manyan laifuka ta Amurka FBI, ta zargi Koriyan da kutse ga kamfanin na Sony, koda yake ba ta bayyana dalilanta game da zargin ba.
An dai yiwa kamfanin na Sony kutse ta yanar gizo ne a karshen watan Nuwambar da ya gabata, lamarin da ya yiwa na'urorin kwamfutar kamfanin babbar illa, ya kuma haddasa dakatar da shirin kamfanin, na fitar da sabon fim din sa mai suna "The Interview", fim din barkwanci, da shirya wanda ke dauke da wani yunkuri na hallaka shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewan.