Sojojin gwamnatin kasar Somaliya suka kashe mayakan kungiyar Al-Shabaab kusan 20 ne tare da raunana wasu 29 a yankin Puntland mai cin gashin kansa dake arewa maso gabashin Somaliya, in ji hukumomin tsaron yankin a ranar Talata.
Abdiweli Mohamed Ali, shugaban yankin Puntland, ya tabbatar da cewa, jami'an tsaron yankin Puntland PDF sun kashe mayakan kungiyar Al-Shabaab 20 da kuma raunana wasu 29 a cikin wani kazamin fada na kwanaki biyu a Galgala, dake shiyyar Bari. Haka kuma jami'an PDF biyar ne suka mutu a yayin wannan gumurzu. (Maman Ada)