Majalissar dokokin kasar Somaliya na shirin amfana da hanyar musaya da hadin gwiwwa da takwaranta na kasar Sin, in ji kakakin majalissar Somaliya Mohammed Osman Jawari tare da jakadar kasar Sin a Somaliya Wei Hongtian a ranar Litinin din nan.
Da yake magana lokacin wata ganawa tsakanin su biyun, Jawari ya jinjina wa ziyarar jakadar kasar Sin a majalissar ya ce, wannan wani babban yunkuri ne na kulla dangon zumunci mai karko tsakanin kasashen biyu, yana mai lura da cewa, Somaliya da Sin sun dade suna amfana da zumunci mai kyau tun samun 'yancin kasar a shekarar ta 1961.
Jakadan na kasar Sin shi ma ya bayyana imanin da yake da shi na cewar, dawo da dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu zai karfafa zumuncin tsakanin al'ummomin bangarorin biyu, kuma zai habaka ci gabansu.
Kasar Sin dai ta bude ofishin jakadancinta a Somaliya tare da aika sabon jakada bayan tsaiko na shekaru 23 tun lokacin da Somaliya ta fada cikin yakin basasa. (Fatimah)