Hukumar tsaron kasar Somaliya a yankin Gedo ta ce, ta ki amincewa da bukatar da kasar Kenya ta nuna ta son a mika mata jagorar kungiyar Al-Shabaab Zakariya Ismail Hersi.
Kanal Abass Ibrahim Gurey wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai ya ce, sun ki amincewa da bukatar abokan aikin nasu da ke kan iyaka da kasar. Jami'an tsaron kasar Kenya dai na cikin rundunar sojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a yankin.
Gurey ya kara da cewa, jagarar mayakan Al-Shabaab din, 'dan asalin kasar Somaliya ne, don haka za'a yi mashi shari'a ne a cikin kasar, inda zai amsa laifuffukan da ake tuhumar sa da su, kuma sojojin Somaliya za su iya mika shi ne kawai ga gwamnatin tarayyar Somaliya a Mogadishu.
Har yanzu babu wata sanarwa da ta fito daga bangaren gwamnatocin Somaliyan da Kenya game da wannan batu.
Kasashen biyu dake makwabtaka da juna suna da hadin gwiwwa na tsaro mai karfi, dalilin hare-haren mayakan Al-Shabaab wadanda ke kai barazana ga tsaron kasashen biyu. (Fatimah)