in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Cape Verde ya ce, Sin abokiyar nahiyar Afirka ce
2014-12-05 14:36:07 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Cape Verde suka bayar a ranar 4 ga wata, an ce, ministan harkokin wajen kasar Jorge Tolentino da har yanzu ke ziyarar aiki a nan birnin Beijing ya bayyana wa 'yan jarida a ranar 3 ga wata cewa, kasar Sin ba ta aiwatar da wani sabon tsarin mulkin mallaka a nahiyar Afirka. Ya ce, Sin abokiyar nahiyar Afirka ce, babu wata kasar dake ikon zargi kasar Sin a wanan fanni ba.

Tolentino ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi alkawarin raya tattalin arziki na nahiyar Afirka da sa kaimi ga bunkasa harkokin dan Adam, ana iya ganin babban ci gaban da aka samu a kasar Cape Verde a wannan fanni. Ya ce, an kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasarsa ta Cape Verde da kasar Sin tun daga lokacin da Cape Verde ta samu 'yancin kai a shekarar 1975. A cikin shekaru 20 da suka gabata, an zurfafa yin mu'amala a tsakanin kasashen biyu a fannonin ala'du da tsaron kasa da sauransu. A halin yanzu, yawan Sinawa dake kasar Cape Verde yana karuwa, yawancinsu matasa ne ko masu kafa kamfanoni, wadanda suka ba da gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Cape Verde. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China