in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Sin ya gana da ministan harkokin wajen Cape Verde
2014-12-02 20:37:06 cri
A yau ne, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya gana da ministan harkokin wajen kasar Cape Verde Jorge Homero Tolentino Araujo a birnin Beijing.

A yayin ganawarsu, Li Yuanchao ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Cape Verde abokan arziki juna ne, kasashen biyu na ci gaba da habaka dangantakar abokantaka dake tsakaninsu cikin zaman lafiya kuma cikin sauri tun lokacin da suka kulla dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu. Haka kuma kasar Sin na son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Cape Verde domin karfafa dadadden zumuncin dake tsakaninsu, inganta harkokin siyasa, da kuma zurfafa hadin gwiwarsu kan ayyukan noma, ayyukan jinya, ba da ilmi, yawon shakatawa da sauran fannoni, ta yadda za a kara inganta dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare kuma, minista Tolentino ya bayyana cewa, jama'ar kasar Cape Verde na daukar jama'ar kasar Sin a matsayin 'yan uwansu, kuma kasarsa na maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin a kasar, da kuma karfafa shawarwarin al'adu dake tsakanin kasashen biyu, da kafa kwalejin Confucius a kasar Cape Verde.

Bugu da kari ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kuma gana da minista Tolentino inda suka sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin da abin ya shafa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China