in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin kammala filin wasanni da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a kasar Cape Verde
2014-08-25 11:02:44 cri

A kwanakin baya aka shirya bikin kammala filin wasanni da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a kasar Cape Verde a Praia, babban birnin kasar.

Firaministan kasar Cape Verde a cikin jawabinsa wajen bikin ya ce, filin wasannin kasar ya kasance daya daga cikin manyan ayyuka da aka gina tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta, abin da zai taimakawa kasar da ta kara samun ci gaba a fannin wasanni.

Sa'an nan ya mika godiya ga gwamnatin kasar Sin, tare da bukatar bangarorin da abin ya shafa da su yi amfani da wannan filin wasanni yadda ya kamata domin a mai da birnin Praia a matsayin wani kayataccen gari a fannin wasanni. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China