Mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya gana da takwaransa na kasar Sudan Mr Hassabu Mohamed Abdul-Rahman a ran 30 ga wata a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Mr Li ya labarta cewa, cikin shekaru 55 da suka gabata tun kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, sun bangarorin 2 suka nace ga amincewa da juna da nuna daidaici tsakaninsu da taimakon juna. Sin ta kan tsaya tsayin daka wajen hangen nesa kan dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, kuma tana fatan zurfafa hadin kai da kasar ta Sudan daga dukkan fannoni. Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuwa, tana fatan kara azama wajen tuntubar juna tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da yin musayar ra'ayi kan matakan daidaita ayyukan kasashensu, da kuma ciyar da dangantakar sada zumunci tsakaninsu gaba.
A nasa bangare, Hassabu Mohamed Abdul-Rahman ya shelanta cewa, kasar Sudan na fatan kara zurfafa dangantakar dake tsakanin jami'yyun kasashen biyu da gwamnatocinsu yadda ya kamata. (Amina)