Wakilin din-din-din na kasar Sin, a MDD Liu Jieyi ya shawarci kasashen duniya da su ba da mahimmanci a wajen ci gaban kasashen Afrika yayin da ake zayyana ajandar ci gaban kasashe a bayan shekara ta 2015.
Liu Jieyi wanda ya gabatar da wannan shawarar, a yayin da yake jawabi ga wani babban taron MDD, ya kara da cewar, ba da fiffiko ga ci gaban Afrika, wani babban bangare ne na hadin kai domin zaburar da ci gaban duniya baki daya.
Liu ya kuma yi kira da samar da ingancin muhalli a Afrika, tare da kara karfafa huldar dangantaka na gudanar da ayyuka tare, kana kuma da girmama darajar Afrika da jama'arta. (Suwaiba)