in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kwashe ma'aikatan ofishin jakadancinta daga Libya
2014-07-27 16:20:52 cri
Amurka ta sanar da debe daukacin ma'aikatan ofishin jakadancinta dake kasar Libya zuwa kasar Tunusiya mai makwaftaka, karkashin kulawar dakarun sojinta.

Hakan dai na zuwa ne a gabar da yanayin tsaro a Tripoli, babban birnin kasar ta Libiya ke ci gaba da tabarbarewa.

A cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Merie Harf, an kwashe kimanin jami'ai 150 daga ofishin jakadancin, sakamakon yadda dakarun sa kai masu hamayya da juna ke ta artabu, da nufin amshe ikon babban filin jiragen saman kasar tun daga ran 13 ga watan nan.

Dakarun dai na daukin ba dadi ne a wani wuri maras nisa da ginin ofishin jakadancin Libiyan dake Tripoli.

Harf ta kara da cewa, ofishin jakadancin Amurka zai ci gaba da ayyukansa kan batutuwan Libya ko dai daga birnin Tunis, ko Washington ko kuma wani wuri a arewacin Afirka.

Rahotanni sun ce wannan fada shi ne mafi muni da birnin Tripoli da ma Benghazi dake gabashin kasar ke fuskanta, tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Gaddafi a shekarar 2011.

Amurka dai na dari-dari da yanayin tsaro a kasar ta Libya, tun bayan da aka hallaka tsohon jakadanta Chris Stevens tare da wasu Amurkawa su 3 a Benghazi, a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2012. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China