Wani kakakin gwamnatin ya sanar da hakan a taron manema labarun da ya gudana a ranar Jumma'a, haka kuma ya nanata cewa, idan aka samu rabuwar kasa, to za a tsunduma al'ummarta cikin wani yanayi na yaki maras karshe, abin da zai janyo barna matuka.
Tun bayan da aka hambarar da mulkin Ghadafi a shekarar 2011, filin saukar jiragen sama dake Tripoli, fadar mulkin kasar, ya fara zama hannun dakarun kungiyar Zintan, wadanda ba su da wata akidar musamman kan addini. Amma daga ranar 13 na watan da muke ciki, wasu kungiyoyin dakaru masu ra'ayin addini, ciki har da kungiyar Misrata, sun fara kai hari ga filin saukar jirgin saman. Zuwa ranar Jumma'a, an riga an kwashe kwanaki 13 ana artabu da juna.
Kungiyoyin 2 da ke arangama da juna, wato Zintan da Misrata, sun kasance kungiyoyin dakaru mafi karfi a kasar Libya. Ganin haka da kuma yadda ake ta samun rikice-rikice a birnin Banghazi dake gabashin kasar, sun sa ana nuna damuwa kan yiwuwar sake abkuwar yakin basasa a kasar ta Libya. (Bello Wang)