Kawo yanzu, babu wata masaniya kan hakikanin yawan mutanen da suka mutu da jikkata. Kwanaki da dama har yanzu hukumar kiwon lafiya ta Libya bata gabatar da alkaluman mutuwar mutane da wadanda suka jikkatar ba a birnin Tripoli.
Tun bayan da aka hambarar da mulkin Gaddafi a shekarar 2011 ya zuwa yanzu, kungiyar Zintan ke mallakar filin jirgin saman Tripoli. Amma daga ranar 13 ga wata, kungiyoyin dakaru da dama, ciki har da kungiyar Misrata, sun fara kai hari kan filin jirgin saman, hakan ya haddasa lalacewar kayayyaki sosai. Daga bisani, kuma aka rufe filin jirgin saman, abin da ke nuna cewa ba za a bude shi cikin gajeren lokaci ba.(Fatima)