Kwamitin tsaron MDD ya bayyana damuwa matuka, game da yawaitar matsalolin tsaro, da na lafiya a kasashen dake yammacin nahiyar Afirka, lamarin da a cewar wakilan majalissar, ya zama wajibi, gamayyar kasashen duniya su gaggauta daukar matakan shawo kan sa, ba tare da wani bata lokaci ba.
Wannan dai batu na kunshe ne cikin wata sanarwar bayan taron majalissar, da aka rabawa 'yan jaridu a jiya Laraba.
Har wa yau, sanarwar ta zayyana cutar nan mai saurin kisa ta Ebola, da barazanar ayyukan tada kayar baya, da mayakan kungiyar Boko Haram ke haifarwa yankunan arewa maso gabashin Najeriya, da ma makwaftan kasar kamar Nijar, da Chadi da Kamaru, a matsayin manyan misalai na halin da wannan yanki ke fuskanta.
Da yake karin haske game da hakan, wakilin musamman na babban magatakardar MDD a yammacin Afirka Said Djinnit, ya ce, likitoci sun yi gargadi game da yiwuwar yaduwar cutar Ebola, ya zuwa wasu karin kasashen dake nahiyar Afirka, da ma wadanda ke nahiyar Turai.
Baya dai ga kasar Guinea inda a karon farko, aka samu bullar cutar tun cikin watan Maris da ya gabata, yanzu haka cutar ta kara yaduwa zuwa kasahen Liberia da Saliyo. Tuni kuma ta lakume rayukan jama'a da yawansu ya kai 481, cikin mutane 779 da aka tabbatar sun kamu da ita.
Game da batun ayyukan ta'addanci kuwa, kwamitin na tsaro ya jinjinawa kwazon wakilin musamman na babban magatakardar MDD a yammacin Afirka, bisa kyakkyawan wakilci, tare da kwazonsa game da yunkurin da mahukuntan Najeriya ke yi, na ganin an sako 'yan matan nan na Chibok, wadanda mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su tun ranar 14 ga watan Afirilun da ya gabata. (Saminu)