in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNEP ta yi gargadi game da amfani da na'urori masu kunshe da sinadarai masu hadari a Afirka
2014-06-13 10:07:47 cri

Wani mai magana da yawun ofishin shirin kare muhalli na MDD UNEP, ya ja hankalin samu cinikayyar na'urorin sanyaya wurare da na sanyaya abinci, da su kauracewa shigar da na'urorin dake kunshe da sinadarai masu gurbata sararin samaniya zuwa kasashen Afirka.

Jami'in wanda ya bayyana hakan a birnin Kigalin kasar Rwanda, yayin taron da shirin na UNEP ya gudanar, ya kuma yi kira da masu amfani da irin wadannan na'urori a nahiyar, da su rage sayen masu dauke da sinadarin HCFC mai rushe garkuwar sararin sama, da aka fi sami da Ozone.

Masana dai na bayyana cewa, na'urorin da ke kunshe da wannan sinadari na HCFC na fidda sinadarai dake rushe wannan rariya ta Ozone, wadda ke da matukar amfani wajen kare hasken rana mai illa ga bil'adama.

Taron dai na wannan lokaci ya samu halartar masu ruwa da tsaki a wannan fanni, da kuma kwararru daga kasashen Afirka 28. An kuma tattauna game da amfani da na'urorin da ba sa dauke da wannan sinadari na HCFC, da kuma yadda ya dace a yi amfani da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China