Sojojin Nigeriya sun samu nasarar kame wani jirgin ruwa mai dauke da kayayyaki da ake amfani da su wajen fasa bututun mai ba bisa doka ba a yankunan dake da arzikin man fetur na kasar tare da kama mutane 9 da ake zargi da hannu a ciki.
Mustapha Anka, kakakin rundunar hadin gwiwwa na JTF a yankin Niger Delta ya ce, jirgin mai dauke da danyen mai da ba'a iya tantance yawan shi ba, sojojin sun kama shi ne a kurdin Mangbiye dake jihar Bayelsa.
Sojojin dai sun aiwatar da bincike a kan masu satan albarkatun mai a wurare da dama cikin kwanaki 10 da suka gabata domin kawo karshen matsalar satan mai a wannan yankin.
A cewar kakakin sojojin da aka tura unguwar Igbematoro a jihar ta Bayelsa sun lalata wajen sarrafa mai ba bisa doka ba guda 23, wurin adana man kuma guda 18, ban da duro duro na mai guda 34 makare da danyen mai da aka sace, da kwale-kwale guda 6, da sannan da injunan na zugo mai daga kasa guda 3. (Fatimah)