Kasar Najeriya ta kammala wasu tsare-tsarenta na amfani da makamashin hasken rana a cikin manyan ayyukan bunkasa hanyoyin wutar lantarki zuwa yankunan karkara, in ji ministan makamashin Najeriya, Chinedu Nebo. Wannan kasa dake yammacin Afrika na aiki tare da masu ruwa da tsaki a wannan fanni domin cimma wannan buri, in ji mista Nebo a yayin wata ziyarar baki na kwalejin tsaro ta kasar Botswana a Abuja, babban birnin kasar.
Haka zalika, ministan ya jaddada cewa, ma'aikatarsa za ta bincike wasu hanyoyi da sanya ido, ta yadda masu amfani da wutar lantarki a wadannan yankuna da shirin ya shafa, da su rika biyan kudaden kulawa da kayyayakin samar da wutar lantarki ta hasken rana. (Maman Ada)