A ranar Alhmamis 25 ga wata ne, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya ce, ya kamata Majalissar da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU su hada hannu wajen kokarin inganta zaman lafiya da cigaba mai dorewa a nahiya Afrika.
Da yake jawabi a wajen wani taron muhawara da majalissar ta yi mai taken "hanyar lumana da za'a warware matsalolin da Afrika ke fuskanta" Mr. Ban ya fadakar da ribar da aka samu ya zuwa yanzu, sannan ya bukaci a kara himma domin a inganta nasarorin da aka samu har ma a wuce gaba.
A ta bakinsa, "Afrika ta yi kokari sosai, gaskiya daya ce kuma dole a fade ta, nahiyar sansanoni ga 7 a cikin 10 na tattalin arzikin duniya da suka fi saurin bunkasa. Sannan yawancin al'ummarta suna karkashin mulkin demokradiya ne." Ya kuma lura da cewa, "Ana samun cigaba sannu a hankali wajen daidaita tsaro da samar da zaman lafiya, kuma rashin tsaro a Mali, Afrika ta tsakiya, kan iyaka na yankunan Hamada, da jamhuriyar demokradiya na Kongo, da ma sauyin mulki ba bisa doka ba na Guinea Bissau ba zai dakushe nasasar da aka samu ba, na cewa, yawan rigingimu a nahiyar ya ragu sosai."
A nashi bayanin lokacin bude taron, shugaban babban taron majalissar Vuk Jeremic, cewa ya yi, dole ne kasashen duniya su mayar da hankalinsu gaba daya a kan matsalolin tsaro masu sarkakkiya da nahiyar take fuskanta, wadanda suka shafi bangaren ta'addanci, sauye-sauye mulki, manyan laifuka da ake shiryawa tsakanin kasashen, karuwan makamai ba bisa izini ba, shimfida ingantaccen zaman lafiya da kuma yawan gudun hijira.(Fatimah)