in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 50 a Borno a farmakin da suka kai
2014-06-10 11:01:14 cri

An kashe mayakan da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram sama da 50, a wani hari da sojojin suka kai a jihar Borno, wacce ke arewa maso gabashin tarayyar Najeriya, inda kuma nan ne, kungiyar ta Boko Haram ta yi kaka-gida.

Kakakin sojojin Najeria, Chris Olukolade ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, sojojin dake yankin sun kuma dakile wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka shirya kaiwa a karshen mako, a kan wasu kauyuka na jihohin Borno da Adamawa.

Sanarwar kakakin sojojin Nigeriyar, ta ce, 'yan ta'addan suna kan hanyarsu ta kai hare-hare ne a kan wasu kauyukan, da ke kan hanyar Bilta a jihar Borno, a inda sai sojojin Najeria suka yi masu kwantan bauna.

Sanarwar ta ce, kungiyar tana muradin kafa shari'ar musulunci a kasar ta Afrika ta yamma, wacce ke amfani da tsarin damokradiyya. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China