Mista Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ana bisa gudanar da shawarwari ta yadda za'a cimma wata yarjejeniya.
Yarjejeniyar za ta samar da wani tsarin daukar niyya domin kara zurfafa huldar dake bisa tushe mai kyau tun da jimawa, in ji mista Ahmed a yayin bajen kolin man fetur da gas na kasashen gabashin Afrika karo na uku, wanda ya samu halartar wakilai fiye da 400 daga kasashe 40.
A shakarar 2011, kasar Kenya da kasar Sudan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya hana rubanya haraji. Mista Ahmed ya bayyana cewa kasarsa da kasar Kenya na gudanar da shawarwari kuma yana fatan samun lasin harkar man fetur a kasar Kenya. (Maman Ada)