Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai, yana mai cewa,gwanatin Sudan ta tattara wadannan alkaluma ne daga ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD(OCHA) a makonni biyu da suka gabata.
Tuni dai shirin samar da abinci na duniya(WFP) da abokan huldar sa suka raba abincin na wata guda ga mutanen da suka kai 8,500. Ya kuma bayyana cewa, kungiyar bayar da agaji ta Red cross da ke Sudan ta kafa kananan asibitocin gaggawa a Rashad, wani gari da ke arewa maso gabashin kudancin Kordafan.(Ibrahim)