An tabbatar da mutuwar mutanen 108 an kuma ceto wadansu 194 sannan sauran kuma sun bace ana kan nemansu, in ji Koh Myun-seok, babban darektan na'urori da fasaha a kan tsaron bakin tekun jiragen ruwan kasar.
Su dai wadanda aka ceto har yanzu ba a samu kari a adadinsu ba na 174. jirgin mai nauyin tan 6,825 ya kife ne tare da nutsewa a tsibirin Jindo dake kudu maso yammacin gabar kasar ta Koriya ta kudu a ranar Laraban da ta gabata yana dauke da mutane 476 da suka hada da daliban makarantar gaba da firamare na Danwon su 325 da kuma malamansu 14. (Fatimah Jibril)