Ya zuwa safiyar ranar Litinin, yawan mutanen da aka tabbatar sun rasu, sakamakon nutsewar wani jirgin ruwan fasinjan kasar Koriya ta Kudu ya kai mutane 64. Yayin da kuma aka tabbatar da ceto jimillar mutane 174.
A cewar kakakin cibiyar aikin ceton mutanen da hadarin ya rutsa da su, ya zuwa rana ta 6 da fara aikin laluben, akwai ragowar mutane 238 da ba a kai ga samun su ba. Ana kuma fatan gaggauta yanayin aikin a wannan lokaci da yanayi ke dada kyautata.
A ranar Lahadi ne dai aka zura wasu manyan igiyoyi, wadanda masu nutso cikin ruwan ke amfani da su, wajen shiga kafofin jirgin da ke can kasan ruwa, domin lalubo sauran mutanen da suka makale a cikin sa. Matakin da ake ganin zai taimaka matuka wajen gaggauta aikin ceton. (Saminu)