Sin da Amurka sun yi musayar ra'ayi kan wasu muhimman batutuwa kan batun nukiliya na Korea ta Arewa
A ranar Talata 29 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta tabbatar da cewa, bisa goron gayyatar Amurka, tawagar Sin ta kai ziyara a kasar a karkashin jagorancin manzon musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin zirin Koriya Wu Dawei, inda aka yi musayar ra'ayi kan sa kaimi ga kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da farfado da shawarwari tsakanin bangarori shida batun nukiliya na kasar Korea ta Arewa tsakanin Sin da Amurka.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku