Shafin internet na Ashrouq da ke Sudan, ya bayar da rahoton cewa, 'yan tawayen dake fafutukar kwatar 'yancin Sudan yankin arewaci (SPLM-N), sun yi luguden wuta da rokoki kan Kadugli, babban birnin jihar kudancin Kordofan, kwana guda bayan dakatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka sanya hannu da gwamnati.
Gwamnan jihar kudancin Kordofan Adam Alfakki, ya bayyana cewa, harin rokokin da 'yan tawayen suka kai ya nuna cewa, ba su da niyyar samar da zaman lafiya a kudancin Kordofan. Don haka ya ce, sojojin Sudan za su ci gaba da daukar tsauraran matakai a yankin, bayan da 'yan tawayen suka kaddamar da matakan soja, sakamakon dage tattaunawar birnin Addis Ababa.
Bayanai na nuna cewa, tun a shekarar 2011 ne 'yan tawayen suke yakar dakarun gwamnati a jihohin Blue Nile da kudancin Kordofan, inda suka kai harin bama-bamai na karshen a tsakiyar watan Disamba.
A ranar Talata ne aka dakatar da tattaunawar da sassan biyu suka fara a farkon watan Fabrairu sakamakon rashin fahimtar da ke tsakaninsu. (Ibrahim)