Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi tir tare da allawadai kan kisan sojojin MDD a yankin Darfur na kasar Sudan.
Shugabar kwamitin tarayyar Afrika, madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta bayyana cewa, ta kadu tare da nuna damuwa sosai kan kisan sojojin kasar Senegal dake cikin tawagar wanzar da zaman lafiya da MDD da AU suka tura wa yankin Darfur cikin hadin gwiwa a yayin wani harin da wasu mutane da ba'a san ko su wadanne ba suka kai a yammacin Darfur a ranar 13 ga watan Oktoba, in ji kungiyar AU.
Makon da ya gabata, wani jami'in sojan kasar Zambiya ne aka daka wa wuka a gidansa wanda kuma wannan ya zama ajalinsa, in ji wannan sanarwa.
Madam Dlamini-Zuma ta soki wadannan ayyukan kisa na rashin imani da ake kaiwa sojojin UNAMID dake salwantar da rayukansu domin kawo zaman lafiya a yankin Darfur.
Shugabar ta kwamitin AU ta jaddada muhimmancin gano wadanda suka tabka wadannan laifuka tare da gurfanar da su gaban kuliya. Haka kuma ta nuna juyayinta da sunan kungiyar AU ga iyalan mamatan, da gwamnatoci da kuma jama'ar kasashen Senegal da Zambiya. (Maman Ada)