Wakilai daga kungiyar AU da na MDD sun bayyana rashin jin dadinsu ga halin tabarbarewar tsaro, tare da karin koma baya da yankin Darfur na kasar Sudan ke ciki a halin yanzu.
Wakilan sun bayyana hakan ne ranar Laraba 23 ga wata, yayin bikin bude taron kwamitin tsaron MDD da aka shirya, don nazartar yanayin da yankin na Darfur ke ciki.
Da yake tsokaci kan wannan lamari, wakilin musamman, kuma jagoran tawagar hadin gwiwar kungiyar AU da tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNAMID Mohammed Ibn Chambas, ya ce, halin tsaro, da barazanar dake fuskantar ayyukan jin kai a Darfur abubuwa ne dake da matukar bukatar sa ido, tare da daukar matakan magance su.
Ibn Chambas ya ce, babbar matsalar dake addabar yankin ba ta wuce rigingimu tsakanin al'ummu, da kabilu mazaunan wurin ba. Yankin na Darfur dai na kunshe da kabilu bakaken fata da Larabawa da ba su ga maciji da juna, wadanda kuma sau da yawa kan faru ma juna bisa rikicin da kan shafi batun mallakar filayen kiwo ko wuraren bayi.
Duk da yunkurin shiga tsakani da sulhunta kabilu mazauna wurin da a kan yi, batun wanzuwar yanayin zaman lafiya ya ci tura. Inda kawo yanzu hare-hare da a kan kaddamar kan tawagogin MDD da na AU ke ci gaba da karuwa.
A ranar 13 ga watan Yulin da ya gabata ma dai sai da aka hallaka jami'an UNAMID su 8, baya ga wasu 16 da suka jikkata a wani wuri daf da Nyala, helkwatar jihar kudancin Darfur. (Saminu)