Jami'an Biyu sun bayyana harin da dakarun na M23 suka kaddamar ga jirgin wanda ba ya dauke da makaman yaki, dake tsaka da gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a matsayin wani mummunan aiki da sam bai dace ba.
Da yake karin haske dongane da aukuwar wannan lamari, mai magana da yawun MDD Martin Nesirky cewa ya yi wannan ne karo na Biyu cikin mako guda da dakarun kungiyar ta M23 suka kaddamar da makamancin wannan hari. Sai dai ya tabbatar da cewa, mutanen dake cikin jirgin sun tsira da rayukansu, kuma harin bai lahanta jirgin ba.
Tuni dai jagoran tawagar MDD ta MONUSCO Martin Kobler ya jaddada aniyar ci gaba da gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankunan jamhuriyar dimokaradiyyar Congon, ciki had da zirga-zirgar jirage masu saukar ungulu.(Saminu)