Taron kwamitin shiyya na kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO reshen Afrika ya bude a ranar Litinin a Brazzaville na kasar Congo bisa taken "zuba jari a fannin kiwon lafiya domin cigaba mai karko". Mahalarta wannan taro za su mai da hankali kan batutuwan da suka hada da kula da lafiyar tsoffin mutane, amfani da kimiyyar kiwon lafiya domin kyautata tsarin kiwon lafiya na kasashen Afrika, karfafa karfin kasashen Afrika wajen kula da kayayyakin likitanci da inganta hanyoyin karfafa amfani da magungunan ba da kulawa da rigakafin cutar Sida. Haka kuma a yayin wannan dandali, ministocin kiwon lafiya na kasashen Afrika 47 za su tattauna kan rahoton ayyukan kungiyar WHO a shiyyar Afrika tsakanin shekarar 2012 da shekarar 2013 da darektan shiyya na WHO, dokta Luis Gomez Sambo zai gabatar, da kuma rahoton aiki na kwamitin kiwon lafiyar mata a nahiyar Afrika, da wani kwamitin manyan jami'ai dake karkashin shugabar kasar Liberiya, madam Ellen Johnson Sirleaf.
Ministocin kuma za su tattauna kan kasafin kudin kungiyar na shekarar 2014 zuwa ta 2015, da batun gyaran fuska da ake yi a wannan hukuma da wasu sauran batutuwa.
Darekta janar ta kungiyar WHO, madam Margaet Chan ta bayyana a yayin wannan taro cewa, ya kamata hanyoyin magance matsalolin kiwon lafiya a bullo da su a nahiyar Afrika, tare da nuna cewa, ya kamata a kafa manufofin siyasa domin taimakawa rage talauci, ta yadda za'a a samar wa mutane aiki da kuma samun kulawa a fannin kiwon lafiya. (Maman Ada)