Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi kiran cewa, baki daya a hana tallen sigari ko harkoki dake da alaka da hakan, inda ta ci gaba da cewa, yadda kamfanonin sigari ke yin tallen sigari ba ji ba gani, ya yi sanadin kasa hakura da shan sigari kuma a kalla mutane miliyan shida ne ke mutuwa a fadin duniya kowace shekara saboda shan sigari.
A cikin sanarwar da aka bayar ranar Alhamis, darektan shiyya na hukumar lafiya ta duniya a yankin yammacin Pacific, Dr Shin Young-soo ya yi tsokaci da manufofin hukumar dangane da shawo kan shan sigari, wacce ta bukaci gwamnatoci a fadin duniya da su dage kan hana tallen sigari da sauran harkoki masu alaka da hakan.
Hukumar ta ci gaba da cewa, hana tallen sigari na da amfani wajen hana mutane shan sigari, kuma yana fadakar da mutane dangane da dabara da yaudara kamfanonin sayar da sigari ke amfani da su wajen tallace tallace na jan hankali.
A fadin duniya baki daya, shan sigari na haifar da cututtuka kamar tarin fuka, cutar daji, cutar hakarkari da zuciya.
Hatta wadanda ba su shan sigari, ba su tsira ba domin mutane sama da dubu 600 suna mutuwa sakamakon shakar hayakin sigari.
Hukumar lafiyan ta yi gargadin cewa, muddin ba'a dau matakai shawo kan lamarin ba, to ko shakka babu, yawan mutane da za su mutu sakamakon illar sigari zai kai sama da miliyan 8 kowace shekara nan da shekarar 2030.(Lami)