Shugaba Xi ya bayar da wani muhimmin rahoto, inda ya bayyana cewa, cikin dogon lokaci, ma'aikatan kungiyoyin likitancin Sin da ke aiki a kasashen ketare sun dauki hakkin da kasa ta rataya musu, ta hanyar gudanar da ayyukansu na harkokin jin kai a duniya, inda suka dukufa wajen ba da taimako ga jama'ar kasashen ketare, ta yadda za'a inganta ayyukan kiwon lafiyar duniya da kuma kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa da kasa.
Ya kuma jadadda cewa, ayyukan da kungiyoyin likitancin Sin ke yi a kasashen ketare na da muhimmanci wajen ci gaban harkokin diflomasiyyar kasa. Shi ya sa, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yi kokari wajen kyautata zaman rayuwar ma'aikatan kungiyoyin da kuma ba da taimako gare su wajen warware matsalolin da suke fuskanta yau da kullum, ta haka, za' a iya kyautata aikin likitanci na kasar Sin a kasashen ketare. (Maryam)