Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana yau Jumma'a 16 ga wata, cewar kasar Sin ta taya Ibrahim Boubacar Keita, dan takarar Jam'iyyar Union murnar zama sabon shugaban kasar Mali, kuma Sin za ta inganta hadin gwiwa tare da sabuwar gwamnatin Mali, a kokarin ciyar da dangantaka a tsakanin kasashen biyu zuwa gaba.
Hong ya kara da cewa, Sin na da imanin cewa, shugaba Keita zai iya jagorantar gwamnatin da kuma jama'ar kasar Mali wajen shimfida zaman lafiya da na karko da kuma samun bunkasuwa a kasar. Ko da yaushe kasar Sin na goyon bayan kasar Mali wajen ganin an samar da zaman lafiya, kuma tana son hada kai tare da kasashen duniya wajen ci gaba da bayar da gudummawa ga aikin samar da kwanciyar hankali da samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Mali.(Kande Gao)