Kasar Sin na fatan za a hanzarta sake yin shawarwari a tsakanin bangarori 6 kan batun nukiliya na Koriya
A ran 23 ga wata da yamma, mamban kwamitin dindindin na hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Liu Yunshan ya gana da Choe Ryong-hae, manzon musamman na Kim Jong-un, shugaban kasar Koriya ta arewa a nan birnin Beijing, inda Liu Yunshan yake fatan bangarori daban daban za su tsaya kan matsayin cimma burin rashin kasancewar nukiliya a yankin Koriya, da kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin, kuma kokarin wareware matsaloli iri iri ta hanyar yin shawarwari. Bugu da kari, ya bukaci a dauki matakan sassauta tsananin halin da ake ciki a yankin Koriya, ta yadda za a iya farfadowa da shawarwari tsakanin bangarori shida a kokarin cimma burin rashin kasancewar nukiliya a yankin Koriya, da tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Asiya.
Bugu da kari, Liu Yunshan ya bayyana cewa, bangaren Sin yana son kara yin ma'amala da bangaren Koriya domin neman matsaya daya kan batutuwa iri iri, ta yadda za a iya raya huldar dake tsakanin kasashen Sin da Koriya ta arewa lami lafiya ba tare da wata tangarda ba.
A nasa bangaren kuma, Mr. Choe Ryong-hae ya ce, dalilin da ya sa babban sakatare Kim Jong-un ya tura shi zuwa kasar Sin a matsayin manzonsa na musamman shi ne kyautata, karfafa da kuma bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu. Bangaren Koriya ya yaba wa bangaren Sin sosai kan gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Koriya, da namijin kokarin da ya yi wajen dawo da yin shawarwari kan batun yankin Koriya zuwa hanyar da ta dace. Bangaren Koriya ya amince da shawarar bangaren Sin ta farfadowar yin shawarwari da bangarori daban daban da abin ya shafa. (Sanusi Chen)