Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying wadda ta sanar da hakan a yau Alhamis 18 lokacin da take zantawa da manema labarai a Birnin Beijing fadar Gwamnatin kasar, ta yi bayanin cewa, ganin babbar hukumar tsaro ta kasar Koriya ta Arewa a yau Alhamis din nan ta lissafa sharuddan da za'a bi in har za'a yi zaman tattaunawa tsakaninta da Amurka da kuma makwabciyarta Koriya ta Kudu game da wannan yanayi da ake ciki na fargaba, akwai bukatar a zauna a tattauna lami lafiya.
Hukumar tsaron kasar Koriya ta Arewa dai a cikin sharuddan da ta bayar ta bukaci Amurka da Koriya ta Kudu da su daina yin kalamai na tsokanar fada, kuma su nemi gafararta game da takalar da suka yi tun da fari, sannan su bada tabbacin cewa, ba za su yi wani garajen da zai tada yaki ba da nufin takalar Koriya ta Arewa.
A game da wadannan sharudda, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki da bangarorin da abin ya shafa da sauran kasashen duniya domin shawarar yadda za'a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya, kuma za ta nace na ganin duka bangarorin 6 sun tattauna an kuma samar da zaman lafiya.
Hua Chunying ta kara da cewa, wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa masu gabashin nahiyar Asiya da kuma ganin yankin zirin Koriya ya kasance ba tare da wani makamin nukiliya ba abu ne da ya zama burin kowa da batun ya shafa kuma nauyi ne a wuyansu.(Fatimah)