A ranar llaraba ne kasar Togo ta hau mukamin shugabancin kwamitin tsaron MDD na karba-karba na watan Mayu.
Wakilin din-din-din na kasar Togo a MDD Kodjo Menan shi ne ya karbi ragamar shugabancin kwamitin daga hannun Eugene-Richard Gasana, jakadan kasar Ruwanda a MDD wanda shi ne ya rike matsayin shugaban kwamitin a watan Aprilu.
Wannan shi ne karo na biyu da kasar Togo ta hau matsayin shugabancin kwamitin tun lokaci da aka zabe ta a matsayin mamba wacce ba ta din-din-din ba ga kwamitin na MDD a cikin watan Oktoban 2011.
Ana yin karba-karba na shugabancin kwamitin tsakanin kasashe dake aiki a kwamitin na zaman lafiya da tsaro kowane wata bisa amfani da jerin harrufan Turanci na sunayen kasashen.(Lami)