A ranar Talata ne babbar kungiyar kwadago ta ma'aikatan gwamnatin kasar Togo ta yi barazanar tafiya yajin aiki ganin cewa, majalisar dokokin kasar ba ta yi na'am kan wani kudurin aikin gwamnati ba, a cikin watan Disamban da ya gabata. Wannan kuduri shi ne zai maye gurbin wanda ake amfani da shi tun shekarar 1968.
An sa rai da cewa, majalisar za ta amince da kudurin, kafin na kasafin kudin shekarar 2013, domin a samu shigar da bukatun ma'aikatan gwamnatin cikin kasafin kudin na wannan shekara da muke ciki na kasar.
A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, shugabannin kungigoyin kwadago guda 6 na ma'aikatan gwamnati, suna nuna rashin jin dadinsu tare kuma da yin kira ga ma'aikata su yi damarar yajin aiki da ba'a taba ganin irinsa ba, a tarihin aikin gwamnati a kasar ta Togo.
Yajin aikin da ake sa ran yi, zai janyo ma'aikatan gwamnati kusan dubu 50 na kasar Togo, wadanda za su nuna kin amincewarsu kan karancin albashin ma'aikata da rashin kyawun yanayin aiki karkashin gwamnatin kasar Togo.(Lami)