Zanga-zangar nuna bacin ran al'ummar kasar Togo a karkashin laimar gungun jam'iyyun adawa da kungiyoyin kare demokaradiyya mai taken "mu ceto Togo" da wannan kawance ya shirya a ranar Laraba, an tarwatsata lamarin da ya janyo ba hamutta iska tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a Lome, babban birnin kasar, in ji kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Daruruwan mutane sun fito kan titunan birnin a rana ta biyu ta zanga-zangar da aka tsara shirya har zuwa kwanaki uku. Amma kuma tun rana ta farko, aka fara samun tashe-tashen hankali a wasu wurare. Manyan hanyoyi dake kai wa tsakiyar birnin da kuma unguwar hukuma sun kasance sansanonin masu zanga-zangar, lamarin da ya janyo tsekon motoci. (Maman Ada)