in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da kungiyar abokantakar al'ummar Sin da Afirka ta Kudu
2013-03-22 10:02:52 cri

A ranar Alhamis 21 ga watan nan ne aka kaddamar da sabuwar kungiyar abokantakar al'ummar kasar Afirka ta Kudu da kasar Sin a birnin Johannesburg, lamarin da ya bude wani sabon shafi ga kyakkyawar dangantakar dake tsakanin bangarorin al'ummun biyu.

Yayin bikin kaddamar da kungiyar wadda aka yi wa lakabi da SACPFA, shugabanta Manne Dipico, ya ce, kungiyar ba wai kawai za ta taimaka wajen inganta musayar fasahar kasuwanci da ci gaban tattalin arzikin al'ummun kasashen biyu ba ne, a'a, har ma da bunkasa musayar al'adu, da karfafa kwarewar juna a fannonin ci gada daban daban. A cewarsa, kungiyar za ta hada kai da ragowar jam'iyyun gama kai, domin cimma burikan da ta sa a gaba.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta SACPFA Cao Xingzhi, cewa ya yi, suna fatan wannan kungiya tasu, za ta zamo wani dandali, da zai ba da damar yin hadin gwiwa tsakanin kwararru a kowane fanni na rayuwa, domin daukaka matsayin cigaban al'ummun kasashen biyu.

Mambobin kungiyar dai sun hada da kwararru a fannonin ayyukan hukuma, da masana, da lauyoyi, 'yan kasuwa, da masu harkar nishadantarwa, likitoci da dai sauransu.

Tun dai shekarar 1998 da aka kulla dangantakar huldodin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, ake ta samun karin ci gaba daga dukkan fannoni, inda ake kuma sa ran kafuwar wannan sabuwar kungiya, zai dada bunkasa wannan sashe.

Bugu da kari, a ranar 26 ga watan Maris din nan, ake sa ran kungiyar ta SACPFA, za ta sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da kungiyar sada zumunta da kasashen ketare ta kasar Sin, domin bunkasa ci gaba a fannonin lafiya, da tattalin arziki, da al'adu, da ilmi da dai sauransu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China