Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Elsevier ya wallafa fassarar littafin kasar Sin game da COVID-19
2020-11-10 09:43:53        cri
Kamfanin Elsevier na kasar Netherlands mai wallafa binciken kimiyya da nazari game da bayanai, wanda kuma ke wallafa mujallar nan ta Lancet, ya wallafa, tare da kaddamar da fassarar turanci, ta littafin kasar Sin mai magana kan cutar numfashi ta COVID-19.

A jiya Litinin ne dai Elsevir, ya kaddamar da littafin mai lakabin "COVID-19: Muhimman hanyoyin kandagarki, kariya da kuma maganin ta " da hadin gwiwar madaba'ar jami'ar Shanghai Jiao Tong.

Cikin wadanda suka buda littafin gabanin wallafa shi, akwai babban masananin kasar Sin game da cututtuka da suka shafi numfashi Zhong Nanshan, kuma ana fatan littafin zai raba dabarun kasar Sin na yaki da COVID-19 ga sauran sassan duniya.

Dukkanin editocin littafin kwararrun masana ne a fannin ilmin likitanci, wadanda kuma suka taba kasancewa kan gaba a aiki da cutar COVID-19. Tuni kuma littafin ya ja hankalin masu ruwa da tsaki a sassan kasa da kasa, jim kadan bayan kaddamar da na Sinancin sa.

Da fari dai littafin rubutu ne na bincike game da hanyoyin kandagarki da na shawo kan cutar COVID-19, wanda masu bincike Sinawa suka gabatarwa kamfanin na Elsevier, kamar dai yadda mahukuntan kamfanin suka tabbatar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China