Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An dakatar da ganawar gaba da gaba a helkwatar MDD dake New York saboda bullar cutar COVID-19
2020-10-28 10:19:30        cri

Daga jiya Talata, helkwatar MDD dake birnin New York, ta dakatar da ganawar gaba da gaba tsakanin jami'an ta, bayan da aka samu rahoton harbuwar jakadun wata kasa su 5 da suka harbu da cutar COVID-19.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin babban magatakardar MDDr Stephane Dujarric, ya ce an sanar da zauren MDD harbuwar walikan wata kasa su 5, cikin kasashe mambobin kwamitin tsaron majalissar 15 da cutar COVID-19. Tuni kuma sashen jami'an lafiya na majalissar ya fara aikin tantance wadanda suka yi cudanya da masu dauke da cutar.

Ko da yake dai Mr. Dujarric bai bayyana kasar masu dauke da cutar ba, amma wasu rahotanni sun ce jami'an 5 'yan asalin janhuriyar Nijar ne, sun kuma halarci zaman kwamitin tsaron MDDr na ranar Alhamis din makon jiya.

A wani sakon email da Mr. Dujarric ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce ya zuwa yammacin jiya Talata, adadin wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a sassan hukumomin MDD ya kai mutum 132, ciki har da jakadun dindindin na wasu kasashe mambobin majalissar su 10, da kuma jami'an ta dake aiki a kasashen waje su 45. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China