2020-10-24 16:46:33 cri |
Ban da wannan kuma, wani binciken da aka yi a watan Satumban bana ya nuna cewa, kashi 9.6% na al'ummar yankin England sun taba kamuwa da kwayoyin cutar COVID-19, kana wannan jimilla ta fi yawa a yankin London, hedkwatar kasar.
Bayan sanar da wannan rahoto, wasu yankunan kasar Birtaniya sun sake kaddamar da matakai mafi tsanani na kandagarkin bazuwar cutar COVID-19.
A sa'i daya, gwamnatin yankin Lombardia dake arewacin kasar Italiya ta yanke shawarar takaita aiwatar da ayyukan tiyata a asibitocin yankin, don magance yiwuwar bazuwar cutar COVID-19. Kana daga yammacin jiya, an sake bude wani asibitin wucin gadi dake cibiyar bajekolin kayayyaki ta Milan, inda ake da niyyar kwantar da wasu mutane 6 da suka harbu da cutar COVID-19, wadanda lafiyarsu ke cikin wani yanayi mai tsanani, a cikin wannan asibitin. Ana sa ran wannan asibiti na wucin gadi zai iya daukar majiyyata 45. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China