Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron kolin MDD zai yi zama na musamman kan yaki da cutar COVID-19 a farkon Disamba
2020-11-06 10:48:48        cri

Babban taron MDD UNGA, ya yanke shawarar gabatar da wani taron musamman a ranar 3 zuwa 4 ga watan Disamba domin zaburar da kasa da kasa game da hadin gwiwar yaki da annobar COVID-19.

Volkan Bozkir, shugaban babban taron MDDr karo na 75 ya ce, taron musamman da MDDr ta gudanar game da yaki da annobar COVID-19 a shekarar 2019 wani muhimmin al'amari ne a tarihi, kuma tamkar gwaji ne, game da hadin gwiwar bangarori daban daban. Za a iya fahimtar hakan ne ta hanyar matakan hadin gwiwar kowane bangare kan wannan babban al'amari da ake fuskanta a duniya, ya bayyana hakan ne gabanin amincewa da shawarwarin da aka bayar a taron musamman na MDD karo na 31 game da batun yaki da annobar ta COVID-19.

Kudirin wanda ya samu amincewar mambobin kasashe 150 da suka halarci babban taron MDDr daga cikin mambobi 193. Babu wata kasa a duniya da ta jefa kuri'ar kin amincewa da kudirin, sai dai kasashen Amurka, da Isra'ila da Armenia sun janye jiki daga jefa kuri'ar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China