Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu dauke da COVID-19 a duniya ya zarce miliyan 50 in ji jami'ar Johns Hopkins
2020-11-09 10:40:50        cri
Alkaluman baya bayan nan da cibiyar binciken kimiyya da aikin injiniya ta jami'ar Johns Hopkins dake Amurka ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa ranar Lahadi, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta harba a duniya baki daya ya zarta miliyan 50.

Cibiyar ta ce ya zuwa ranar ta Lahadi, mutane 50,052,204 sun harbu da cutar, kana ta yi sanadiyyar rasuwar mutum 1,253,110 a sassan duniya daban daban.

Amurka ce ke kan gaba da yawan wadanda cutar ta hallaka, inda a kasar kadai, COVID-19 ta kama mutane 9,879,323, kana ta hallaka mutane 237,192. India ce ke biye da Amurka a yawan masu harbuwa da cutar da mutum 8,507,754. Kasar Brazil ce ta uku da yawan masu dauke da cutar 5,653,561, kana ta hallaka mutane 162,269, adadin da shi ne na biyu a duniya baki daya.

Alkaluman sun kuma bayyana cewa, akwai karin mutane da suka haura su miliyan 1.1 a kasashen Rasha, da Faransa, da Sifaniya, da Argentina, da Birtaniya da Colombia. A daya bangaren kuma, kasashen da cutar ta hallaka mutane sama da 40,000 sun hada da India, da Mexico, da Birtaniya, da Italy da Faransa.

A ranar 17 ga watan Satumba ne adadin masu dauke da wannan cuta ya kai miliyan 30, kana adadin ya karu zuwa miliyan 40 a ranar 19 ga watan Oktoba. Kaza lika cikin kwanaki 32 adadin masu harbuwa da cutar a sassan duniya baki daya, ya haura daga mutum miliyan 30 zuwa miliyan 40, ya kuma kara karuwa daga miliyan 40 zuwa miliyan 50 cikin kwanaki 20. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China