Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rukunin likitoci na Sin mai aiki na gajeren lokaci ya tashi zuwa kasar Gambiya
2020-11-09 14:23:08        cri
Bisa gayyatar da gwamnatin kasar Gambiya ta yi, rukunin likitoci na Sin mai aiki na gajeren lokaci, wanda lardin Liaoning ya tura, ya tashi daga birnin Shenyang a jiya zuwa kasar Gambiya, don gudanar da ayyukan bada jinya har na tsawon watanni uku. Wannan karon ma Sin ta kara tura rukunin likitoci ga kasashen waje, bayan da ta tura rukunin masana na yaki da cutar COVID-19.

Rukunin likitoci na Sin a wannan karo ya kunshi membobi 9, wadanda suke kula da ilmin bada jinya ga mutanen da suka kamu da cututtuka masu tsanani, da cututtuka masu yaduwa, da bada jinya ga marasa lafiya, da magance cututtuka da sauransu, kuma za su shiga asibitocin kasar Gambiya don bada horo, da bada jinya ga mutane masu fama da cutar COVID-19.

Haka zalika kuma, rukunin likitocin na Sin da zai yi aiki a kasar Gambiya karo na 4, zai tashi tare da rukunin likitoci na Sin mai aikin gajeren lokaci zuwa kasar ta Gambiya, don gudanar da ayyukan likitanci har na tsawon shekara daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China